Muryar Amurka (VOA) ta fitar da fim din tarihin ta'adancin kungiyar Boko Haram a birnin New York

July 2024 · 2 minute read

- VOA ta fitar da sabuwar fim din da ya bayyana irin baranar da kungiyar Boko Haram ta yi a Najeriya

- Fim din Boko Haram da VOA ta fitar ya bayyana irin gudunmawar da wasu mutane suka bada wajen ganin cewa rikicin Boko haram ya zo karshe

Gidan jaridar Muryar Amurka na Hausa(VOA) ta fitar da sabuwar fim din tarihin kungiyar Boko haram mai taken “Mugun tafiya” inda ta bayyana irin azabtarwa da kissan gilla da kungiyar ke yi a ranar Laraba 24 ga watan Janairu, 2018 a birnin New York.

Mutane daga kowane bangare na rayuwa sun hallara a ofishin jakadancin kasar Amurka dan kallon wannan sabuwar fim a birnin, New York.

Fim din mai tsawon sa’oi biyu da gidan jaridar VOA ta fitar ya ba da cikakken bayyanai akan yadda ta’addancin Boko Haram ya fara da illar da suka yiwa arewa maso gabashin Najeriya.

Fim din ya ba da labarin mutane da ta’adancin Boko haram ya canza rayuwan su da nazarin da gwamnati ke yi wajen dawo dasu cikin hayacin su.

KU KARANTA : Kungiyar 'yan tawayen da ke yiwa gwamnatin Libya biyayya sun kama mutanen dake azabtar da ‘yan gudun hijira

Fima din ya bayyana gudunmuwa da hastarin da wasu suka sa rayukansu dan ganin rikicin Boko haram ya zo karshe wanda ya hada da labarin wata matashiya mai sunan Aisha sarauniyyar mafarauta.

Gudunmawar da Aisha sarauniyyar mafarauta ta bada yasa an kama mayakar kungiyar boko haram da dama a dajin Sambisa da kuma ceto mutanen da suke yi garkuwa da su wanda ya kunshi mata da kananan yara.

An kuma bayyana irin gudunmawar da kungiyar masu fafutikar neman dawo da ‘yan matan Chibok (BBGOG) da aka yi awon gaba da su a shekara 2014.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kG1va2xjYrq2vtiaqWaZnaq%2FrK2Mr6aaZaSWeqe105qpZpyRYrOquYydoKdlpJa%2FqrTIp2StmZGZrq%2BvyKdkpK2enLa6rdFmmaijn2K1or7ApmSaZZKev6%2B1zWalnq9drryzt42hq6ak