- Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya fara kokarin gyara gwamnatinsa da nufin mayar da ita kan kudirinsa na inganta rayuwar al'umma
- Fasto Eno ya tsige kwamishinan ayyuka na musamman, Bassey Okon daga muƙaminsa, ya umarci ya bar ofis nan take
- Sakataren gwamnatin jihar Akwa Ibom, Prince Enobong Uwah ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, 10 ga watan Yuni, 2024
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya kori kwamishinan ayyuka na musamman a gwamnatinsa, Bassey Okon.
Sakataren gwamnatin jihar, Prince Enobong Uwah ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Litinin, 10 ga watan Yuni.
Gwamnan Adamawa ya yiwa gwamnatinsa garambawul, an sauya wasu kwamishinoni
Prince Uwah ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne a wani ɓangare na kokarin sake fasalin gwamnatin jihar Akwa Ibom ta bi layin manufar gwamna, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin korar kwamishina a Akwa Ibom
"Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya sauke Dokta Bassey. P, Okon, kwamishinan ayyuka na musamman daga matsayin 'dan majalisar zartarwa ta jihar nan take.""Mai girma gwamna ya gode masa bisa irin ayyukan da ya yiwa jihar tare da yi masa fatan alheri a dukkan abubuwan da zai tunkara nan gaba.“Bisa haka, ana umurtarsa da ya mika mulki ga babban sakatare a ma’aikatar. A yanzu dai sakataren gwamnatin jihar ne zai kula da ma’aikatar har sai an nada sabon kwamishina."- Prince Uwah.
A bisa wannan mataki, Okon ya zama shi ne kwamishinan farko da Gwamna Eno ya kora daga aiki, rahoton Vanguard.
Gwamna Zulum ya mika mulkin jihar Borno ga mataimakinsa, ya fadi dalili
Ana raɗe-raɗin cewa gwamnan na fuskantar matsin lamba daga masu ruwa da tsaki kan ya yi garambuwal a majalisar zartarwarsa saboda galibi ya gaje su ne daga tsohon gwamna.
Kotu ta yanke hukunci kan ƴan majlaisa 27
A wani rahoton kuma babbar kotun jihar Ribas ta ce har yanzun ƴan majalisa 27 karƙashin jagorancin Martin Amaewhuke 'ya 'yan jam'iyyar PDP ne.
Da yake yanke hukunci ranar Litinin, Mai Shari'a Okogbule Gbasam Okogbule Gbasam ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da sun koma APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6gpZsamafp5a6r62MrpuoZamWeqy70aJkpK%2BRora0tMinmKdlka7GtrfAZqWaZZ2qwKK5zJqlZpldlri4rYyimailXw%3D%3D